fbpx
Tuesday, May 18
Shadow

Masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da ‘yan kasuwa 7 a Nasarawa

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu satar mutane ne sun sace’ yan kasuwa bakwai, wadanda suka hada da mata uku da maza hudu yayin da suke dawowa daga Kasuwar Kauyen Ugya, a karamar Hukumar Toto da ke Jihar Nasarawa.

Wani direba, wanda ya tsere daga harin, Ibrahim Saidu, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 6:12 na yamma a ranar Talata.
Ya ce masu garkuwan sun fara bude wa motarsa ​​wuta ne kuma suka fasa daya daga cikin tayoyinsa, amma ya samu nasarar tserewa.
Abun takaici, an afkawa motar da ke bayansa, wacce kuma ke dauke da ‘yan kasuwa daga Kasuwar Kauyen Ugya zuwa garin Toto.
Ya ce direban Volkswagen Golf, wanda ke dauke da ‘yan kasuwar, ba zato ba tsammani ya rasa yadda zai yi sai ya nufi cikin daji, wanda ya ce masu garkuwar sun zo suka yi awon gaba da su suka nufi daji da bindiga.
Kakakin rundunar ‘yan sanda ta Jihar Nasarawa, ASP Ramhan Nansel, ya ce ba shi da masaniya game da lamarin satar mutanen.
Ya ce zai tuntubi jami’in ‘yan sanda na shiyyar (DPO) da ke karamar hukumar domin tabbatar da faruwar lamarin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *