fbpx
Tuesday, August 3
Shadow

Mata da yara sun yi Zanga-Zangar rashin tsaro a Zamfara

A Najeriya, ‘Yan sanda a jihar Zamfara sun ce sun kama mutum talatin da shida a cikin masu zanga-zangar da suka tare babban titin zuwa Sokoto don nuna fushinsu kan karuwar hare-haren ‘yan fashin daji a yankunansu.

Bayanai sun ce masu zanga-zangar akasarinsu mata da yara kanana sun tare titin Gusau zuwa Sokoto tsawon sa’o’i tun da safiyar Alhamis. Mutanen sun fusata ne saboda kazancewar hare-hare a kauyukansu.

Wasu da BBC ta zanta da su ta waya sun ce hari na baya-bayan nan da ‘yan bindiga suka kai ya shafi kauyuka fiye da bakwai a yankin Bungudu ciki har da Marke da Burai da Bingi da Gurgurau da Landai.

‘Yan sanda sun ce sun yi amfani da hanyoyin da doka ta amince wajen tarwatsa masu zanga-zangar da suka ki jin lallashi. Sai dai shaidu sun ce hayaki mai sa hawaye da ‘yan sandan suka harba ya galabaitar da yara da dama.

Wani mazaunin yankin na karamar hukumar Bungudu ya ce harin ‘yan fashin na wayewar garin jiya Alhamis ne ya harzuka su, sakamakon kashe mutum 19, da kwashe musu dabbobi.

Har ma a cewarsu ya yi sanadin mutuwar wasu., kamar yadda daya daga cikinsu wanda ya ce ba sai an ambaci sunansa ba, ya shaidawa BBC.

”Ka na cikin kauye ko daji, da abincin ka da dabbobin ka, amma an zo an kone ma ka kayan abinci, dabbobin an kwashe ta ina za ka zauna, domin haka mata da yara da maza su ka fito tituna su na zanga-zanga, shigowar ‘yan sanda suka harba hayaki mai sa hawaye suka tarwatsa masu zanga-zanga. Kuma lamarin ya janyo mutuwar akalla yara 7 sanadiyyar hayaki mai sa hawaye da kuma tafiyar wahala da aka yi da su.”

Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar Zamfara SP Muhammad Shehu dai ya musanta zargin mutuwar wasu masu zanga-zangar. A cewarsa ko kwarzane babu wanda ya ji a lokacin tarwatsa sun.

”Ba gaskiya ba ne, babu wanda ya ji ko kwarzane lokacin da aka bude hanyar bare kuma mutuwa. Mun yi kokarin amfani da hanyoyin da suka da ce don tabbatar da an bude hanyar, kuma mun kama sama da mutum 30, an fara gudanar da bincike domin sanin dalilin da ya sa suke yawan zanga-zanga a wannan yankin,” inji SP Muhammad Shehu.

Mutane da dama ne zanga-zangar ta katsewa harkokinsu na tafiye-tafiye. Direbobi sun rika sauke fasinjojin da suka dauko saboda babu hanyar da za su wuce kasancewar an datse hanyar da za su wuce tsawon sa’o’i.

Ko a makon jiya ma sai da al’ummar garin Bingi cikin karamar hukumar Maru suka yi makamaciyar wannan zanga-zangar, saboda zargin da suka yi cewa za a kwashe wasu jami’an tsaro a yankinsu, ko da yake hukumomi sunce ba dauke su za a yi ba illa dai za a maye gurbinsu da wasu ne.

BBChausa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *