fbpx
Sunday, September 26
Shadow

Mata me ‘ya’ya 10 ta koka da cewa, tayi-tayi da mijinta su yi tsarin iyali amma yace sai sun haifi yara 22

 

Wata mata me yara 10 da koka da yawan haihuwar da take. Tace ta baiwa mijinta shawarar su yi tsarin iyali amma yaki yadda.

 

Tace yace mata sai ya haifi yara 22.

 

Matar me shekaru 30, Gentrix Wekesa dake Kakamega County na kasar Kenya ta bayyana cewa, yanzu haka tana da ciki na 11.

 

Tace al’ada na daya daga cikin abinda ya hana mijin nata yadda da tsarin iyali. A hirar da aka yi da ita a TV 47 tace duk shekara si ta haihu kuma dan autanta yanzu bai kai shekara daya ba amma gata da wani tsohon ciki.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *