fbpx
Monday, November 29
Shadow

Matar da kewa mijinta dukan kawo wuka saboda ya kasa mata Ciki

Wata mata me shekaru 32, Chinwendu Chita ta rika lakawad mijinta, Okechukwu Chita dukan kawo wuka saboda ya kasa Yi mata ciki ta haihu.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Matar ta koka da cewa sun shafe shekaru da yawa tare da mijin nata amma har yanzu ya kasa mata ciki abinda ya isheta. Lamarin ya farune a, Lamari  ya farune a layin Alhaji Agbeke dake, Ago Okota dake Legas.

Tun daga shekarar 2018 lamarin ke faruwa wanda hakan yasa,Okechukwu har yake tsoron komawa gidansa. ‘Yan Sandan yakin na Ago sun sha shiga lamarin su raba fada kuma matar ta yi alkawarin ta daina dukan mijin nata amma daga baya ta ci gaba.

A karshen shekarar 2019 ne Chiwendu ta kulle daki tawa mijin nata duka har ta buga mai ludayin So ye a ka sannan kuma ta kwace mai kudi har Naira Dubu 650.

A ranar Litinin ne Chiwendu tawa Mijin nata dukan kawo wuka inda ya kwace da kyar ya kuma garzaya Wajan ‘yan sanda, nan aka turo wata ‘yar sanda dan ta tafi da ita, nan ma tawa ‘yar sandan duka. Daga baya dai an samu kamata kuma aka gurfanar da ita gaban kotu,kamar yanda PM News ta ruwaito.

Ana Zargin Chiwendu ta yiwa mijinta da jami’ar ‘yar sanda duka, zargin da duka ta karyata. Saidai Alkali ya bayar da belinta akan Naira Dubu 700 sannan kuma da mutane 2 da zasu tsaya mata.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *