fbpx
Thursday, September 23
Shadow

Matar Gamnan Kano, Farfesa Hafsat Ganduje ta yi burus da gayyatar EFCC

A ranar Alhamis din makon da ya gabata ne, EFCC suka gayyaci matar Gwamnan Kano, Farfesa Hafsat Abdullahi Umar Ganduje kan zargin aikata ba daidai ba.

 

Danta, Abdulaziz ne ya kaita kara wajan EFCC din kamar yanda Premium times ta ruwaito.

 

Yayi zargin cewa tana amfani da matsayin iyalainsu wajan arzuta kanta.

 

Majiyar ta yi kokarin jin ta bakin gwamnan inda ta tuntubi kakakin gwamnatin, Mohammed Garba, amma yace bai san da maganar ba.

 

Shima kakakin EFCC, Wilson Uwujaren ya ce baisan da maganar ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *