fbpx
Thursday, September 23
Shadow

Matasa biyar sun mutu yayin da suke dauko gawar dan uwansu da ya mutu a sanadiyyar cutar kwalara daga Legas zuwa Sokoto

Wasu matasa biyar sun mutu yayin da suke kai gawar dan uwansu wanda ya mutu sakamakon cutar kwalara a jihar Legas zuwa Sokoto.

Mamatan yan ci rani ne dake zau ne a jihar Legas inda suke neman abincin su.

Kamar yadda Aminiya ta ruwaito, suna zaune ne a Ojota, yankin da aka ce ya fi fama da cutar kwalara a jihar Legas.

Wata majiya ta bayyana cewa; Bayan rasuwar abokin nasu, sun yanke shawarar kawo gawarsa garinsu, Sanyinna a karamar hukumar Tambuwal ta jihar Sokoto don binne shi.

Sun kuma tattauna da wata motar bas dake zuwa Sakkwato kuma a kan hanyarsu mutane biyar sun kamu da cutar kuma sun mutu kafin isowar su.

Wasu fasinjoji guda biyar a halin yanzu suna karbar magani a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Farko ta Sanyinna. Ba a bar motar ta shiga cikin garin ba.

Ardon Sanyinna, Alhaji Shehu Abubakar wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce marigayin ya tafi ci rani ne a Legas.

An yi jana’izar mamatan kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Kalli hotunan jana’izar a kasa..

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *