fbpx
Thursday, September 23
Shadow

Matasa masu hidimar kasa 5 sun mutu a hanyar Katsina, Shugaba Buhari yayi Jimami

SHUGABA BUHARI YAYI BAƘIN CIKI SAKAMAKON RASUWAR MATASA BIYAR 5 MASU SHIRIN YIWA ƘASA HIDIMA DA SUKA RIGAMU GIDAN GASKIYA.

Fassara: Hon. Buhari Sallau Hadimin Shugaban kasa Muhammadu Buhari Bangaren Rediyo da Talabijin.

Shugaba Muhammadu Buhari yaji baƙin ciki sosai na Rasuwar masu shirin Yiwa Ƙasa Hidima a sanadin Hatsarin Mota ranar Laraba 28 ga watan Yuni, 2021, a babbar hanyar Abuja Kwale dake birnin Tarayya.

Shugaban yabi sahun Hukuma da Hukumomin gudanarwa da Ma’aikatan Hukumar Yiwa Ƙasa Hidima NYSC, Gurin yin addu’ar bankwana ga wadan da suka rasa Rayukan su a Mumunar Hatsarin.

Shugaban yayi alhini ga Iyalan Matasan, ya bada tabbaci cewa, Ƴan Najeriya sunaji kunci na halin ɓakin ciki da suke ciki, da kuma ci gaba da yi musu addu’a a yayin wannan lokaci mawuyaci da suke ciki.

Shugaban ya miƙa sakon fatan Alkhairi ga daukacin membobin Matasa masu Yiwa Ƙasa Hidima, dama kuma Sabbin wanda suke shirin zuwa sansanonin Yiwa Ƙasa Hidima dake a Fadin Kasa.

Shugaba Buhari, ya kara jaddada cewa Jindadi da tsaron wadan nan Matasa Ƴan Najeriya, wanda sukayi biyayya na kiran Bauta wa kasa da zuciya guda batare da son kai ba, zasu ci gaba da samun kulawa daga Gwamnati, Baza’a taba mancewa da sadaukarwan da Matasa wadan da suka riga mu gidan gaskiya ba.

Femi Adesina:
Mashawar ci Na Musamman ga Shugaban Kasa a Fannin Yada Labaru da Wayar da kan Jama’a.
29 ga watan Yuni, 2021.

 

Matasan sun rasu ne a hanyar su ta zuwa Jihar Katsina inda a canne aka aikasu su yi bautar kasar.

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *