fbpx
Tuesday, June 15
Shadow

Matasan Arewa sun zabi Gwamna Bala Muhammad a matsayin dan takarar Shugaban kasa a 2023

Ka Fito Takarar Shugaban Kasa A 2023 Ko Kuma Mu Yi Maka Ritaya Daga Siyasa, Sakon Kungiyar Matasan Arewa Ga Gwamna Bala

Wata kungiyar matasan Arewa mai suna “Northern Youth Leadership Forum (NYLF) ta gargadi Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulkadir Mohammed da ya fito takarar shuganban kasa a zaben 2023 ko kuma su yi masa ritaya daga harkar siyasa.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a yayin taron da ta gudanar a garin Yola babban birnin jihar Adamawa a yau Laraba, inda aka zabi Gwamna Bala a matsayin dan takarar ta hanyar kada kuri’a.

Kimanin daliget 450 ne suka halarci taron tare da kada kuri’ar su ga mutane biyun da kungiyar ke son su fito takara, wato Gwamna Bala Mohammed (Kauran Bauchi) da shugaban gidan talabijin na AIT, wato Cif Raymond Dokpesi.

A yayin zaben Gwamna Bala ya samu daruruwan kuri’u, yayin da Dokpesi ya samu kuri’u ashirin da takwas.

A yayin da shugaban kungiyar Kwamred Elliot Afiyo yake jawabi, ya bayyana cewa sun kudiri aniyar fitar da dan takarar ne a cikin makonni biyu bayan zaman da suka yi kafin wannan.

Kwamred Elliot ya kara da cewa kungiyar su za ta yi fito-na-fito da Gwamna Bala don ganin sun kawo karshen siyasar sa idan har bai amsa kiran na su na tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023 ba.

“Gwamna Bala ba shi da wani zabi face ya amince da bukatar mu ta ya fito takara shugaban kasa a zaben 2023.

“Ba wai barazana muke yi masa ba, amma ya sani idan har bai amince da bukatar mu ba za mu kawo masa nakasu a siyasar sa, ta hanyar yakarsa a siyasance idan har bai kawo mana wasu kwararan hujjojin da za su hana shi amsa bukatar ta mu ba”, cewar shugaban Kungiyar ta NYLF, Kwamred Elliot.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *