fbpx
Monday, November 29
Shadow

Matashi ya rasu wajen gyara wutar lantarki a Jigawa


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Wani matashi a kauyen Gamsarka da ke Karamar Hukumar Auyo a Jihar Jigawa mai suna Muhammad Bulala ya gamu da ajalinsa a ranar Litinin da ta gabata sakamakon sauke masa wutar lantarki da ma’aikatan Kamfanin Lantarki na  Kano (KEDCO) suka yi, inda ya hau turken lantarki zai mayar da wutar da kansa, inda ya rasu nan take.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Jigawa SP Audu Jinjiri ya tabbatar da faruwar lamarin.

Bayanai sun nuna cewa, Bulala ba ya biyan kudin wuta lantarki ne, shi ya sa aka  datse masa wayar wutar gidansa.

Da aka kai mamacin Babban Asibitin Auyo domin duba ko yana da sauran numfashi, sai likitoci suka tabbatar da mutuwarsa, kafin a mika gawarsa ga ’yan uwansa domin yi masa jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *