fbpx
Thursday, September 23
Shadow

Matashiyar da ‘yan uwanta suka kashe ta a Indiya saboda ta saka wandon jins

A ‘yan kwanakin nan ana yawan samun rahotannin ‘yan mata da danginsu ke yi musu duka a Indiya. Hakan ya bayyana ƙarara irin halin da mata da ‘yan mata ke ciki a gidajensu.

A makon da ya gabata ne aka samu rahoton yadda ‘yan uwan Neha Paswan mai shekara 17 suka lakaɗa mata duka har lahira a jihar Uttar Pradesh da ke arewacin Indiya saboda ba sa son yadda take saka wandon jins.

Mahaifiyarta mai suna Shakuntala Devi Paswan ta faɗa wa BBC Hindi cewa an yi wa ‘yarta duka sosai da sanduna bayan kakanninta da kawunnai sun gama muhawara a gidansu da ke ƙauyen Savreji Kharg – ɗaya daga cikin garuruwa marasa ci gaba a jihar.

“Ta yi dogon azumi a ranar. Da yamma, ta saka wandon jins da ‘yar riga kuma ta yi ibadarta. Lokacin da kakanninta suka hana ta sakawa sai ta ce ai an yi wandon ne don a saka kuma sai ta saka,” a cewar mahaifiyarta.

Shakuntala ta ce bayan ‘yarta ta sume sai surikanta suka kirawo adaidaita sahu suka za su kai ta asibiti.

“Ba su bari na raka su ba saboda haka sai na faɗa wa ‘yan uwana, waɗanda suka je asibitin yankin nemanta amma ba su ganta ba.”

Washe gari, Shakuntala ta ce, sai aka samu rahoton cewa an ga gawar wata yarinya a wata gada da ke kogin Gandak. Lokacin da suka je sai suka ga gawar Neha ce.

‘Yan sanda sun shigar da mutum 10 ƙara bisa laifin kisan kai da kuma lalata shaida, ciki har da kakannin Neha da kawunnanta da ‘yan uwanta da wani direba. Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton waɗanda ake zargin ba su ce komai ba.

Wani babban jami’in ɗan sanda, Shriyash Tripathi, ya faɗa wa BBC Hindi cewa suna ci gaba da neman sauran waɗanda ake zargin.

Mahaifin Neha, Amarnath Paswan, lebura ne a Ludhiana – wani gari a Punjab – kuma yanzu ya dawo gida domin ya fuskanci abin da yake faruwa. Ya ce yana aiki tuƙuru domin ya saka ‘ya’yansa a makaranta, ciki har da Neha.

Shakuntala Devi ta ce ‘yarsu ta so ta zama ‘yar sanda, “amma yanzu ba za ta taɓa cika burinta ba”.

Ta yi zargin cewa surikanta sun sha matsa wa Neha ta bar karatu, har ma sukan tsangwame ta duk sanda ta saka wata sutura ba kayan gargajiya ba.

Neha na son ta saka kayan zamani – biyu daga cikin hotunan da iyayenta suka nuna wa BBC sun nuna ta cikin doguwar riga a guda ɗaya, sai kuma wandon jins da riga a ɗayan.

Masu kare haƙƙi na cewa cin zarafin mata da ‘yan mata a al’ummar da maza suka fi rinjaye na ƙaruwa sosai.

Mata da ‘yan mata a Indiya mna fuskantar barazana iri-iri – akan zubar da cikinsu tun kafin a haife su saboda ba a son haihuwar mata – sannan akan nuna musu wariya. A misali na tsakatsakai, ana kashe mace 20 kullum idan aka ba su sadakin aure maras yawa.

Mata da ‘yan mata na zaune cikin tsauraran dokoki a ƙauyukan Indiya, ta yadda a lokuta da dama hakimai da ‘yan uwansu ne ke zaɓa musu suturar da za su saka ko mutanen da za su yi magana da su, sanna duk sanda suka yi wani kuskure ana ganin tsokana ce kuma sai an hukunta su.

A watan da ya gabata wani bidiyo ya ɓulla inda aka ga wani uba yana jibgar ‘yarsa mai shekara 20 tare da wasu ‘yan uwansa a jihar Madhya Pradesh.

Bayan nuna ɓacin rai, ‘yan sanda sun ƙaddamar da bincike inda suka ce mazajen na “hukunta ta” ne saboda ta gudu daga gidan auren da ake “cin zarafinta”.

Mako ɗaya kafin haka, an ga wasu mata biyu iyayensu da ‘yan uwansu na jan su a ƙasa riƙe da gashinsu tare da dukansu da sanduna saboda an kama su suna waya da wani namiji a garin Dhar. Bayan ɓullar bidiyon ‘yan sanda sun kama mutum bakwai.

Kazalika, wani bidiyon daga yankin Gujarat ya nuna wasu maza kusan 15 na dukan wasu ‘yan mata saboda sun yi waya, a cewar ‘yan sanda.

Wata mai fafutikar kare haƙƙin mata, Rolly Shivhare, ta ce “abin mamaki ne yadda muke kashewa tare da dukan ‘yan mata a ƙarni na 21 saboda sun saka wandon jins ko kuma yin waya da samari”.

BBChausa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *