fbpx
Monday, May 10
Shadow

Matsalar Tsaro: Gwamnatin jihar Zamfara ta hana sayar da fetur ta bayan fage, ta kuma gargadi gidajen mai

Gwamnatin jihar Zamfara karkashin jagorancin Gwamna Bello Matawalle ta hana sayar da man fetur a yankunan da suka yi kamari a harakar tsaro ‘yan kwanakin nan a jihar.

Umarnin na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Kwamishinan yada labarai, Alhaji Ibrahim Dosara, wanda ya fitar a Gusau a ranar Asabar.

Kwamishinan ya bayyana cewa an dauki matakan ne bisa ga kokarin da gwamnatin jihar Zamfara ke yi don magance matsalar hare-haren ‘yan ta’addan da ya dabaibaye jihar.”

Kwamishinan ya lissafa sunayen yankunan da abin ya shafa kamar haka: Wanke, Magami, Dansadau, Dangulbi, Dankurmi, Bindin, Munhaye, Kizarah, Kunchin Kalgo da kewaye.

Ya bayyana cewa haramcin zai fara aiki ne nan take kuma zai ci gaba har zuwa wani lokaci.

Ya kara da cewa dole ne yan bunburutu su daina sayar da mai ko su fuskanci fushin hukuma.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *