fbpx
Monday, September 27
Shadow

Matsalar Tsaro: Mun dawo daga rakiyar gwamnati, addu’ace zata fisshemu>>Al’ummar Kaduna

Wasu jama’ar Kaduna sun bayyana cewa sun dawo daga rakiyar Gwamnati kan matsalar tsaro inda suka ce sun rungumi Addu’a.

 

Hakan na zuwane bayan da ‘yan binsuka sace daliban makarantar Bethel a Kaduna.

 

Daya daga cikin iyayen daliban, Esther Joseph ta bayyana cewa, har yanzu diyarta bata dawo daidai ba tun bayan da aka sako ta daga hannun ‘yan Bindigar.

 

Tace diyar tata tana rika yin sambatu. Ta kara da cewa sai da ta biya Naira 500,000 kudin fansa sannan aka sako mata diyarta, amma hukumomi sun bayyana cewa ba’a biya kudin fansa wajan sako dalibanba.

 

Da yawan iyayen daliban sun koma Addu’a maimakon dogaro da gwamnati ta dawo musu da ‘ya’yansu kamar yanda Punchng ta ruwaito.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *