fbpx
Wednesday, December 1
Shadow

Mauludi Son Annabi Ne, Kuma Duk Zuciyar Dake Son Annabi SAW Ba Za Ta Shiga Wuta Ba>>Sheikh Nuru Khalid

Mauludi Son Annabi Ne, Kuma Duk Zuciyar Dake Son Annabi SAW Ba Za Ta Shiga Wuta Ba, Cewar Sheikh Nuru Khalid

Daga Zaharaddeen Gandu

Shahararren malamin Addinin Islama, Sheikh Nuru Khalid limamin masallacin Apo dake Abuja ya halarci maulidin Annabi Muhammadu SAW a garin Mararaban Abuja da jihar Nasarawa duk da cewa malamin ‘dan Aqee’dar Salafiyya ne amma ya halarci maulidin ya kuma hau mimbarin wa’azi tare da fadakar da juna Cewa Kan mahimmanci soyayyar fiyayyan halitta SAW inda malamin yace “duk zuciyar dake son Annabi Muhammadu SAW ba zata Shiga wuta ba”.

Lalle hasashe ya tabbatar da nuni da cewa yana son ya haɗa kan musulmai ne, duk da kasancewar shehin malamin ɗan Salafiyya ne, amma ya karɓi gayyata zuwa wajen Maulidin Annabi Muhammadu SAW

Sannan ya kuma yi wa’azi tare da bayyana mahimmancin haɗin kan Al’umma musilmai, musamman a wannan yanayi da Musilmai ke cikin ƙalubale.

Ba a saba ganin wani malami daga ɓangaren Salafiyya Izalah sun halarci bikin maulidin Annabi Muhammadu SAW ba, duba da cewa ya saɓawa Aqee’darsu. Amma zuwan malamin wajen taron maulidin ya sa Jama’a da dama tofa albarkacin bakin su.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *