fbpx
Thursday, September 23
Shadow

Me kudin Duniya na kokarin kirkiro na’urar da zata hana tsufa

Me kudin Duniya, Jeff Bezos na zuba jari dan ganin an samar da na’urar da zata karawa mutane yawan shekaru zuwa akalla 50 kamin su mutu.

 

Ana kirkirar wannan na’urar ne a Silicon valley wadda kamfanin Altos Lab ke jagoranta.

 

Kamfanin ya tattaro masana daga jami’o’in Duniya dan binciken yanda za’a hana mutane tsufa.

 

Masu kudin Duniya da yawa ne suka zuba jari a wannan kamfani dan a samar da wannan bincike.

 

Saidai an bayyana cewa sakamakon binciken zai dauki shekaru kamin ya bayyana.

 

A shekarun baya dai wani kamfani yayi kokarin samar da irin wannan abu na hana tsufa wanda aka zubawa bera.

 

Beran ya fara dawowa yaro amma kuma sai wata mummunar cuta da ba’a san kalarta ba sameshi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *