fbpx
Friday, January 21
Shadow

Me Ya Hana Kwankwaso Da Abba Tarbar Matsahin Da Ya Yo Tattaki Daga Katsina Zuwa Kano A Kafa Dominsu?

Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso yayi watsi da
Matashin nan da ya yi tattaki daga jihar Katsina zuwa Kano don taya shi alhinin rashin nasara a kotun koli.

Yanzu haka matashin nan dan shekaru 31 da haihuwa, Comr. Aminu Aliyu Tanko, wanda aka fi sani da (AAT) ya yi tattaki har na tsawon kilomita 175 daga jihar Katsina zuwa Kano don ganawa da tsohon gwamnan Kano kuma tsohon Sanatan Kano ta tsakiya, Rabi’u Musa Kwankwaso ya iso jihar Kano.
Comr. AAT, wanda dan asalin jihar Katsina ne, ya yi tattakin kwanaki hudu akan hanya daga ranar Talata 4 ga watan Fabrairun 2020, ya kuma iso Kano a ranar Asabar 8 ga watan Fabrairun 2020 da misalin karfe 4:50 na yamma.
Matashin yace, ya yi tattaki zuwa Kano ne domin taya Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, da dan takarar gwamnan Kano a jam’iyyar  PDP Engr. Abba Kabir Yusuf alhinin rashin nasara da suka yi a shari’ar zaben gwamna a kotun kolin Najeriya. 
A cewar matashin da ya yi tattakin bai sami tarba daga wajen mabiya darikar Kwankwasiyya da kuma Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso ba.
Matashin dai ya biyo ta unguwar Rijiyar Lemu ne dake karamar hukumar Ungoggo zuwa ofishin dan takarar gwamna, Engr. Abba Kabir Yusuf dake karamar hukumar Nasarawa Kano shi kadai tare da wani abokin sa guda daya sai ‘yan jaridu, babu wani dan Kwankwasiyya ko wani makusan ci ga Kwankwaso da ya tarbe shi.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *