fbpx
Thursday, December 2
Shadow

Messi ka iya komawa Juventus su yi wasa tare da Ronaldo

Rahotanni sada Italiya sun bayyana cewa akwai yiyuwar kungiyar kwallon kafa ta Juventus ta dauko tauraron dan kwallon Barcelona, Lionel Messi su buga wasa tare da babban abokin takararshi, Cristiano Ronaldo.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Rahoton da Tuttosport ta ruwaito tace Akwai yiyuwar Messi ya bar Barcelona.

Hakan ka iya tabbata lura da rashin jituwar data fito fili tsakanin Messin da daraktan wasanni na Barcelona, Eric Abidal.

Wani tsohon ma’aikacin Barcelona ya bayyana cewa abune me wuya ace Messi ya bar Barcelona amma ba abude da za’a ce ba zai iya faruwa ba.

Tun messi na dan shekaru 13 ya ke a Barcelona kuma har yayi iyali yanzu yana kungiyar.

Majiyar taci gaba da cewa idan Messi zai bar Barca to zai koma kodai Ingila ko kuma Italiya kuma a Italiyama kungiyoyi 2 ne kawai zai iya bugawa wasa watau Inter ko kuma Juventus.

A ingilama akwai rade-radin dake cewa Messi ka iya komawa Manchester United ko kuma Manchester City.

Saidai abin ji ga duk kungiyar dake son daukar dan wasan shine albashinsa wanda a shekara ya kai fan sama da fan miliyan 80.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *