fbpx
Monday, November 29
Shadow

Messi ya caccaki daraktan wasanni Abidal

Lionel Messi ya caccaki daraktan wasanni Eric Abidal, wanda ya ce ‘yan wasa ba su saka kwazo karkashin tsohon koci Ernesto Valverde ba.

A cikin watan Janairu Barcelona ta kori Valverde ta kuma maye gurbinsa da Quique Setien.
Abidal tsohon abokin kwallon Messi ya fada jawabinsa a wata hira da ya yi da jaridar Spaniya, Diario Sports.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

A ranar Talata Messi ya mayar da martani ”Idan kayi batu kan ‘yan wasa sai ka kama suna, saboda idan ba haka ba za ka samar da kafar fadin da ba haka yake ba.”

An kori Valverde a lokacin da Barcelona ke ta daya a kan teburin La Liga, Real Madrid wadda ta ke ta biyu a lokacin, yanzu ta zama ta daya.

Messi ya kara da cewar ”’Yan wasa ne keda alhakin dukkan abinda ya faru a cikin fili, kuma mune na farko da muke daukar kaddara idan ba mu taka rawar gani ba.

”Ya kamaka fannin wasannin kungiyar shi ma ya dauki alhakin dukkan abubuwan da ke faruwa da kuma hukuncin da ya dauka.”

A hirar da aka yi da Abidal a Diario Sports ya ce ”Ina jin Messi yana jin dadin zama a Barca an kuma tanaki sabuwar kunshin yarjejeniya da ake tattaunawa da dan wasan.”


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *