fbpx
Monday, November 29
Shadow

Messi zai ci gaba da zama a Barcelona>>Guardiola

Pep Guardiola ya kawar da hasashen cewa dan wasan gaban Barcelona da ya taba horaswa zai bar kungiyar don hadewa da shi a Machester City.

Messi mai shekara 31 ya soma buga kwallo a kungiyar kuma har yanzu bai taba sauya sheka ba, sai dai a yanzu yana da damar barin kungiyar ba tare da yarjejeniya ba a karshen kakar wasa ta bana.
Guardiola ya taba horas da Messi a Barca tsakanin 2008 zuwa 2012, kuma sun ci kofin La Liga da na gasar zakarun turai biyu.
Sai dai ya bar kungiyar inda ya koma Bayern Munich bayan da ya zama kocin Barcelona mafi samun nasara a tarihi da lashe kofuna 14.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ya sake barin Munich zuwa Barcelona inda a can ma ya ci kofin Premier biyu tare da Manchester City, ko da yake a baya kungiyarsa na biye wa Liverpool wacce ke mataki na daya da maki 22.

Messi, wanda ya taba zama gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya har sau shida, ya lashe kofi goma a gasar lig-lig kuma gasar zakarun turai sau hudu, kuma har yanzu yana da ragowar lokaci a kwantaragin sa da ake sa ran zai kare a 2021.

A farkon makon nan ne ya mayarwa da daraktan kwallon kafa na Barcelona Eric Abidal martani, bayan ya zargi dan wasan da rashin zagewa a filin wasa.

Kungiyar na biyewa Real Madrid a saman teburin Laligar Spaniya da tazarar maki uku, sai dai Guardiola ya ki cewa komai a kan takaddamar da ke tsakanin mutanen biyu a matsayin su na tsofaffin ‘yan wasansa lokacin da yake horar da Barcelona.

”Ina ji a can zai gama sana’arsa ta kwallon kafa,” in ji Guardiola.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *