fbpx
Thursday, August 5
Shadow

Mijina Mugune, Naira 20 kacal yake bamu ni da yara idan zai fita>>Mata ta gayawa kotu

Kotun dake Mapo Ibadan jihar Oyo, ta kashe aure tsakanin Alimat Onaolapo da mijinta, Biliamin saboda kasa rike gidansa da yayi.

 

Ta bayyanawa kotun cewa, mijin nata ya kasa kula da ita da yaransu 2. Tace kudin da yake bata na abinci basu taba wuce Naira 20 ba.

 

Matar tace yaran su biyu data haifa duka mininta bai kashe komai na kudin Asibiti ba, sai ‘yan uwanta ne suka taimaka mata, tace shekaru shida bayan da ta aureshi, bata ci gaba ba a rayuwarta, tana nan inda take.

 

Dan hakane take neman a raba aurensu, Saidai mijin ya musanta ikirarin matar nasa inda yace  yana kula da ita kuma yana sonta har yanzu. Alkalin kotun, Ademola Odunade ya kashe auren inda yace mijin ya rika baiwa matar Dubu 10 duk wata dan kula da yaransu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *