fbpx
Tuesday, June 15
Shadow

Miliyan 700 za’a kashe wajan biyan Manjan janarorin Soji 29 da za’a sallama daga aikin hakkokinsu

Hukumar Sojojin Najeriya zata kashe Naira Miliyan 700 Wajan biyan kudin Sallama ga Manjan Janarori 29 da za’a sallama daga aiki dalilin nada sabon Shugaban sojoji, Janar Farouk Yahaya.

 

Doka ta yanadi cewa janarorij da za’a wa ritaya, za’a basu kyautar sabuwar Peugeot Motar 508 da me dafa abinci, da masu gadi 2, da dogari 1 da direba 1.

 

Akwai kuma dala $15,000 da za’a rika biyansu duk shekara a matsayin kudin duba lafiyarsu a Najeriya ko kuma a kasar waje.

 

Janarorin tuni suka tafi hutun ajiye aiki. Jimullar kudin motocin da za’a sai musu sun kai miliyan 464, sai kuma sauran abubuwan da za’a musu da darajarsu ta kai ta Miyan 200.

 

Rahoton Sahara Reports yace, wasu daga cikin Janarorin na ta kamun kafa dan a barsu su ci gaba da aiki amma kuma dole doka zata yi aikinta.

Maj Generals J.O Olawumi from Ekiti, J.O Akomolafe from Kwara, C.O. Ude from Enugu, J. Oyefesobi from Ogun, M.O Uzoh from Abia, C.C. Okonkwo from Imo, M.S.A Aliyu from Zamfara, U.M Muhammed from Niger and B.M Shafa from Ogun.”

Others are; “N.E. Angbazo from Nasarawa, Y.P. Auta from Kebbi, A.S. Maikobi from Bauchi, B. Ahanotu from Anambra, S.A. Yaro from Bauchi, J. Sarham from Kano, H.E. Ayamasaowei from Bayelsa, O.F. Azinta from Enugu, B.A Akinroluyo from Ondo, KAY Isiyaku from Niger, AT Haman from Borno, A.M. Aliyu from Gombe, H. P. Z. Vintekaba from Taraba, K.O. The Kadiri from Lagos, and IM Yusuf from Yobe.”

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *