fbpx
Wednesday, December 1
Shadow

MTN na rabawa ‘yan Najeriya Data kyauta: Ka samu taka kuwa?

Kamfanin sadarwa na MTN ya raba wa kwastamominsa katin waya da data kyauta a matsayin diyya sakamakon matsalar da ya samu a makon da ya gabata.

Shugaban kamfanin MTN ne Karl Toriola ya tura wa masu amfani da MTN saƙon a ranar Lahadi tare da wani adireshin YouTube inda ya nemi afuwa kan katsewar sadarwa da ya samu.

Sakon na cewa “an dawo maka da katinka na waya da kuma data da ka yi amfani tsakanin 12 zuwa 7 na yamma.

A cikin sakon, shugaban MTN ya ce injiniyoyin kamfanin sun fahimci cewa an samu matsalar ne daga wata tangardar na’ura da ta mayar da kwastamomi daga tsarin 4G zuwa 3G wanda ya haifar da katsewar layukan na MTN.

Ya ce yanzu an magance matsalar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *