fbpx
Tuesday, May 11
Shadow

Mu bama bukatar kudin sayen makamai sai dai mu kera su – IPOB ta fadawa DSS

Kungiyar yan asalin Biafra (IPOB) sun ce suke kera makamansu a cikin gida.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin da take musanta zargin da Hukumar tsaro ta farin kaya keyi na cewa IPOB na shirin kai hari ga bankuna don samun kudin siyan makamai.

Kungiyar tace bata da wani bukatar kudi don sayen makamai saboda sun da masu kera masu makamai a nan cikin gida Nageriya.

Kungiyar ta kara da cewa jami’an tsaron IPOB ba masu aikata laifuka ne ba, kuma zata dauki kwakkwaran matakai ga duk wasu yan ta’adda masu kokarin bata masu suna.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *