fbpx
Tuesday, June 15
Shadow

Mu bamu ce zamu daina kawo muku man fetur ba sai kune zaku ce kun daina kawo mana Albasa?>>Reno Omokri

Hadimin Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan,  watau Reno Omkri ya caccaki ‘yan kasuwar Albasa da suka ce zasu daina kai Albasa kudu saboda hare-haren da ake kai musu.

 

‘Yan kasuwar sun bayyana cewa an kashe musu mutane 3 sannan sun tafka Asarar Biliyan 4.5. Sun ce idan ba’a daina ba, zasu dsina kai Albasar Kudu.

 

Saidai a martaninsa, Omokri ya bayyana cewa, kasar Isra’ila na da girman kasa Kilometres 22,145 amma suna ciyar da kansu kuma suna daga cikin kasashen da suka fi fitar da abinci zuwa kasashen waje.

 

Yace Girman kasar Kudu ya nunka na kasar Isra’ila sau 10 dan haka wannan barazana, kalubale ne a garesu na su tashi tsaye wajan noma abinda zasu ci.

 

Yace shin a kudu ne kadai ake kashe-kashe, ba’a yi a Arewa? Yace su ba su yi barzanar daina kaiwa Arewa man Fetur ba zai Arewa ce zata ce zata daina kaiwa Kudu Abin? Yace an fi kashe mutane a Arewa fiye da kudu.

Israel has a land mass of 22,145 km. yet, they feed themselves and are a major exporter of food. Southern Nigeria’s land mass is more than 10 times the size of the State of Israel. We must not let anyone use a blockade of onion and tomato to threaten us. That is an insult. Let it be a challenge to us to grow what we eat! Southern Nigeria must brace up and become prosumers: People who consume what they produce. Southerners are being slaughtered all over the North in their tens EVERYDAY, yet we have not threatened to cut off oil and gas supplies to the North. Are our lives less valuable than Northern lives? It is very insensitive to act as if killings only happen in the South. More killings occur up North!

#KeepItOn #TableShaker

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *