fbpx
Thursday, July 29
Shadow

Mu yan Arewa mu ne matsalar kanmu – Gwamna Matawalle

Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle Maradun, ya mayar da martani ga masu kira ga a tsige shi saboda sauya shekarsa.

Matawalle ya kuma yi watsi da jita-jitar cewa ya sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (PDP) saboda yana son ya kara hawa kujerar Gwamna a karo na biyu.

Matawalle ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da DW Hausa a Gusau, babban birnin jihar.

A kan yunkurin PDP na sanya shi rasa kujerarsa, Matawalle ya ce: “Ba ni ne gwamna na farko da ya sauya sheka zuwa wata jam’iyyar ba.

Amma abin da ya kamata ku fahimta a nan shi ne, mu yan arewa mu ne matsalar kanmu. Wannan shine dalilin da yasa zaka ga mulki yana gab da ficewa daga yankin.

Wannan saboda duk wadanda suke kiran kansu shugabannin arewa azzalumai ne kuma mayaudara.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

1 Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *