fbpx
Saturday, December 4
Shadow

Mufa matashin daya kai hari cocin Kaduna Muhammad yace mana sunanshi ba Nathaniel ba>>Kungiyar Kiristoci ta CAN

Duk da hirar da manema labarai suka yi da matashinnan da yayi yunkurin tada bam a cocin Living Faith dake Kaduna kuma da bakinshi ya tabbatar da cewa shi ba musilmi bane kuma sunansa Nathaniel Samuel amma kungiyar Kiristocin Najeriya, CAN ta dage akan cewa sunan Matashin Muhammad Sani


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Shugaban kungiyar ta CAN a jihar Kaduna, John Hayab ne ya tabbatarwa da Punch da wannan batu inda yace bari in gaya muku gaskiya, jami’an tsaron cocine suka fara kama matashin kamin ‘yansanda su zo.

Kuma tambayoyin da suka masa ya gaya musu cewa shi sunanshi Muhammad Sani ba Nathaniel ba kamar yanda ‘yansanda suka Ruwaito.

Ya kara da cewa daga komawar matashin hannun ‘yansanda sai kuma suka ji cewa ya canja suna zuwa Nathaniel Samuel.

Ya kara da cewa wannan lamari ya tabbatar da maganar kasar Amurka na hana ‘yan Najeriya Shiga kasarta dan kuwa Najeriyar bata da cikakken rumbun adana bayanai na ‘yan kasa wanda hakan ke bayar da wahala wajan tantance masu laifi.

Ya kara da cewa kuma maganar kasar Amurkar na saka Najeriya cikin kasashen dake fama da ta’addanci ta tabbata.

Hayab ya ce yanzu ai bama maganar addini ko sunan wanda ya kai harin ake ba. Abinda ake magana shine yayi yumkurin tada bam wanda harine na ta’addanci.

Yace kuma akwai kiristoci masu sunan Musulmi hakanan akwai musulmi masu anfani da sunan Kiristoci.

Ya kara da cewa abin mamakone yanda aka so tayar da Bam din a daidai lokacin da kiristocin ke zanga-zanga akan matsalar tsaro.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *