fbpx
Tuesday, August 3
Shadow

Muhammadu Sanusi II: Ba ni da ra’ayin tsayawa takarar siyasa a Najeriya

Tsohon Sarkin Kano kuma sabon Khalifan darikar Tijjaniyya a Najeriya Muhammadu Sanusi na biyu ya ce ba shi da ra’ayin neman wani mukami a ƙasar, sai dai ya ce zai ci gaba da faɗakar da al’umma a kan irin shugabannin da suka cancanta a zaɓa.

Muhammadu Sanusi na biyu, wanda ya bayyana hakan a wani taron Mukaddimai da kuma Shaihunnai na darikar a karon farko tun bayan naɗa shi mukamin Khalifan, ya ce wannan ra’ayin nasa ba yana nufin ya shiga siyasa ba ne.

A cewarsa, “Idan muna da waɗanda muka amince muka ce za su yi wa al’umma aiki za su gyara ƙasa, sai a hadu wuri ɗaya a taimaka musu – wannan ba shiga siyasa ba ne aiki ne na gyaran ƙasa da gyaran al’umma”.

Ya ce rashin yin hakan na iya jefa mutanen Najeriya cikin babban haɗari da ƙalubale.

Ya kuma ce wajibi sai an bayar da fifiko wajen samar da ilimi musamman ga kananan yara kafin a iya magance matsalolin da ƙasar ke ciki.

“Idan babu ilimin nan, yaran nan da muke ganinsu ba mu sa su a makaranta ba, yayan wadansu kabilu suna can suna makaranta, nan gaba wadan nan yaran sune za sukafa kamfanoni, yaranmu su zama leburorinsu,” in ji Muhammadu Sanusi na biyu.

Sai dai wasu daga cikin malaman da suka halarci wannan taron irinsu, Sheikh Halliru Maraya na ganin duk da irin wadannan shawarwari ko matakai, akwai bukatar a hada da addu’o’i.

Ya ce akwai bukatar mutane su kara jin tsoron Allah sannan a ganinsa, yana mai karawa da cewa ya kamata mahukunta su kare rayuka da dukiyoyin al’umma tare da samar musu da walwala.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *