fbpx
Monday, September 27
Shadow

Muhimmaci da Amfanin kuka ga lafiyar Dan Adam

Bishiyar kuka tanada sinadarai masu yawa ,akwai Vitamin C, da Kuma Calsiom, da Kuma Vitamin B, bayan haka awani bincike na masana ya nuna cewa kuka takan zuko sinadarai da kanta sama da Kala 118.
kuma takan ajiye ruwa acikin ta wanda take tarawa Akalla sama da lita 25000 zuwa Lita 40000 kai har zuwa dari.
Don haka ada akace idan aka rasa ruwa alokacin da akan fasa kuka domin amfani da wannan ruwan, kuma akace Giwaye idan suka rasa ruwan sha acikin daji, kuka suke fasawa suna shan wannan ruwan.
To bayan haka masana sun tabbatar dacewa wannan ruwan, ruwane mai albarka domin yana dauke da cikakken sinadarin mai inganta lafiyar jikin dan adam, daga wasu manyan cutuka
Kamar ciwon Canser.
Hypertension.
Ciwon suga.
Ciwon Asama.
Da dai sauransu, don haka wani Malamin muslunci masani tafusakar magungunan gargajiya, kuma masani kan abinda yashafi kiwon Lafiya na Likitan turai,  yayi bincike cewa to idan baa sami wannan ruwan ba! Wacce Hanya Zaa bi asame shi, yace zaa iya sassako jikin ta, sai awanke ajika, akalla duk rana asha kofi daya.
Bayan haka idan aka hada garin kuka da zuma aka sha akalka cokali daya to yana magance guba wanda aka sha.
Idan kuma aka sha to ko kasha wani Mai cutarwa bazai yi taasiri ba.
Insha Allahu Zamu cigaba da kawo Cigaban Amfanin Kuka ga Lafiyar Dan Adam.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *