fbpx
Tuesday, May 11
Shadow

Mun fara komawa jihar Kano>>Fulani makiyaya

Shugaban Fulani makiyaya kuma Sakataren kungiyar Miyetti Allah, MACBAN, a jihar Kano, Zubairu Ibrahim, ya bayyana cewa makiyaya daga Kudu maso Yamma, Kudu Maso Gabas da wasu sassan kasar sun nuna sha’awar sake komawa RUGA ta Kano.

A cewar Ibrahim, wasu daga cikin makiyayan sun fito daga jihohi irin su Nasarawa, Neja, Enugu, Oyo, da sauransu.
Ya ce tuni makiyaya daga jihohi biyar na tarayyar suka koma Kano.
“Muna da wasu Fulani makiyaya daga Kebbi, Zamfara, Kaduna, Sokoto, da kuma Jigawa wadanda yanzu suke Kano,” in ji Ibrahim daga jaridar Vanguard.
“Gwamnan ya gayyaci duk wanda yake so ya zauna a RUGA ya zo. Idan suka zo kuma mutanen kirki ne, ba abin da zai hana mu karbarsu.
“Abin da ya kamata su yi shi ne bin dokoki da dokokin gwamnati. Yakamata su tafi kiwo da rana ba da daddare ba. Babu abin da zai hana su zuwa idan suna da sha’awa.
“Tunda gwamnan jihar Ondo ya je kafafen yada labarai cewa su (makiyaya) su bar yankin, maimakon su tsaya a wurin sai su bar su fice don kar wani abu mara kyau ya same su da dukiyoyinsu. Kamata ya yi su bar wurin don kare lafiyar su. ”
A kwanakin baya ne Gwamna Abdullahi Ganduje na Jihar Kano ya bayyana cewa ba abin yarda ba ne yanzu ga makiyaya su kwashe dabbobinsu daga Arewa zuwa Kudu.
Ganduje ya bayyana hakan ne lokacin da yake kira ga gwamnati da ta takaita zirga-zirgar makiyaya da shanu daga Arewa zuwa wani yankin na Najeriya.
Ganduje ya bayyana cewa wannan zai kawo karshen yawan rikici tsakanin makiyaya da manoma a kasar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *