fbpx
Monday, November 29
Shadow

Mun Fi Malaman Addini Isar Da Saƙo Zuwa Ga Al’umma>>Inji Ado Gwanja

Shahararren mawaki kuma jarumi a masana’antar shirya fina finan Hausa ta Kannywood Ado Isa Gwanja ya bayya cewa, saƙonsu yana ishewa fiye da na Malamai.

“Ana yarda da mu ana kallonmu, kuma ana sauraronmu fiye da yadda akewa Malamai, sabida a halin yanzu mutane sunfi karkata ga harkar nishaɗi fiye da jin wa’azi.”

“Saboda haka mafita kawai shine a daina ƙyamatar harkar fim, Malamai su shigo ciki domin a Musuluntar da harkar yadda za ta dace da addini da kuma al’adarmu.” Inji shi

Gwanja ya ƙara da cewar, haka Ilimin boko, Malamanmu na wancan lokaci da kuma mutanen kirki suka dinga ƙyamatarsa, aka bar harkar a matsayin kafirci, sai ya zamana mafi yawan waɗanda suke Ilimin a wancan lokacin basu da Ilimin addini sai gashi a yanzu susuke mulkar al’umma.

“Haka ma maganar ‘Film Village’ maimakon a bari a yi shi a Kano inyaso sai a shigo da Malamai da Hisbah cikin lamarin gudun kar a dinga wani abu da bai dace ba, amma sai aka hana gabaɗay, to idan aka yi shi a wata jihar maƙociyar Kano fa? Kaga abinda ake gudu dole shi zai faru, maimakon a yi shi a kano a Musuluntar da shi kaga aka yi shi a Kaduna baza a Musuluntar da shi ba, kuma dole zai shafi ƴan Kano.” Inji Gwanja

Kamar yanda muka sako muku daga kafar Idon Mikiya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

1 Comment

 • KABIRU MUHAMMED BELLO

  ALLAH NA GANIN.
  KASANI KA KABAR MUGUN TARIHIN
  DA HAR ABADA GA ZURIYAR KA
  TA ZAMANKA DAN DAUDU DA BATA YARA MAZA DA MATA ALLAH YA ISAR MA
  MUSULUNCI DA MUSULMI,

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *