fbpx
Thursday, April 22
Shadow

Mun Gamsu da hukuncin Kotu, An fasa Mukabala da Sheikh Abduljabbar>>Gwamnatin Kano

Gwamnatin Kano ta bayyana gamsuwa da hukuncin da wata kotun majistre a jihar ta yanke na hana yin muƙabala, wato zaman tattaunawa da fitaccen malamin addinin musuluncin nan dake jihar Sheikh Nasiru Kabara.

Ranar Jumma’a ne kotun ta yanke wannan hukunci, kasa da sa’a 48 kafin gudanar da muƙabalar da aka jima ana jira.

Hukuncin ya buƙaci a tsaya a kan hukuncin da kotun ta yanke tun a ranar 8 ga watan Fabrairu, wanda ya haɗar da haramtawa Sheikh Abduljabbar yin wa’azi a jihar ta Kano.

Yayin wata zantawa da BBC, kwamishinan watsa labarai na Kano Muhammadu Garba, ya ce bayan tattaunawa da gwamnati ta yi da ma’aikatar shari’a, sun gamsu da wannan hukunci, don haka an fasa yin muƙabalar da aka shirya gudanarwa a ranar Lahadin nan.

BBC ta tambaye shi a kan zargin da wasu ke yi na cewa gwamnatin Kano na da hannu a shigar da ƙarar da aka yi don hana wannan zama, saboda yadda sarkin Musulmi ya ce baya goyon bayan a yi shi, inda ya ce kwata kwata wannan zargi ba gaskiya bane.

Ya ƙara da cewa ko da an ɗaukaka ƙara daga baya wata kotun ta ce a gudanar da zaman, sai gwamnatin Kano ta sake yin karatun ta-nutsu tukunna kafin duba yiwuwar yin hakan.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *