fbpx
Thursday, December 2
Shadow

Mun gano ana daukar ma’aikata a boye>>Majalisar Tarayya

Majalisar Dattijai ta bayyana cewa ta gano ana daukar ma’aikata a boye a ma’aikatun gwamnatin tarayya.

 

Majalisar tace hakan na faruwane duk da yake akwai ikirarin da hukumomin ke yi na cewa, wai shugaban kasa ya hana daukar sabbin ma’aikata.

 

Sanata Danjuma La’a wanda shine shugaban kwamitin raba daidai na mukaman gwamnati q majalisar ya bayyana haka.

 

Yace sun nemi ma’aikatun gwamnati da su kara kudaden da suke kashewa kan ma’aikata dan dai a samu a dauki matasa aiki.

 

Yace akwai matasa da suka kammala karatu shekaru 15 da suka gabata amma har yanzu basu da aikin yi, yace hakan ya taimaka wajan kara yawan matsalar tsaron da ake fama da ita.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *