fbpx
Wednesday, October 20
Shadow

Mun kama masu ba da bayanai ga ‘yan bindiga 2,000 – Gwamnatin jihar Zamafara

Gwamnatin jihar Zamfara ta ce an kama sama da mutane 2,000 da ake zargi da kaiwa ‘yan bindiga bayani tun lokacin da ta yanke dokar hana sadarwa da kara hare-haren sojoji a jihar.

Kwamishinan Yada Labarai na jihar, Ibrahim Dosara ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai ran
Alhamis.

Jami’in ya ce wadanda ake zargin sun bayar da muhimman bayanai kan ayyukansu da kuma yadda ake zargin wasu manyan mutane sun tallafa musu.

Ya ce an samu nasarar ayyukan tsaro a jihar, ya kara da cewa ‘yan ta’adda da yawa sun tsere daga jihar, wasu na fama da yunwa ko tilasta musu su ci danyen abinci sakamakon takunkumin da gwamnati ta saka musu.

“Sun yanke shawarar yin amfani da rakumai don aikata tashin hankali,” in ji Mista Dosara.

Mazauna jihohin, wadanda a kullum suke ba da rahoton irin wahalar da suka sha tare da ‘yan bindigar, ba sa iya samun damar yin magana kan abubuwan da suka faru a yanzu saboda rufe ayyukan sadarwa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *