fbpx
Wednesday, May 12
Shadow

Mun kashe Kwamandojin Boko Haram 18 da sauran mayakan Kungiyar, Babban Limaminsu ma da kyar ya sha>>Sojojin Najeriya

Sojojin Najeriya sun bayyana cewa sun kashe Kwamandojin Boko Haram 18 da wasu mayakan kungiyar.

 

Hakan na zuwa daga kakakin Soiojin ne, Janar Muhammad Yarima. Yace Boko Haram din sun koma garin Damasak ne dan neman daukar fansa a Ranar Alhamis, Inda suka gamu da gamonsu a hannun sojoji.

 

Boko Haram din sun kuma kai hari Gajiram wanda shima bai yi nasara ba.

 

Saidai Yerima yace a harin ranar 11 ga watan Afrilu. Sojoji 3 da wasu farar hula sun rasa rayukansu. Yace amma a ruwan bamabamai da jirgin yakin soji yawa Boko Haram a Marte da Ngala ya kashe manya-manyan shuwagabannin kungiyar inda babban limamin ISWAP din ma da kyar ya sha.

 

Ya bayar da sunayen wanda suka kashe da. Mohammad Fulloja, Ameer Mallam Bello, Ba’a kaka Tunkushe, Abu Muktar Al -Ansari, Ameer Abba Kaka, Abu Huzaifa, Ameer Modu Kwayem, sai Goni Mustapha wanda shine babban Limamin ISWAP da ya aha da kyar.

 

“The deadly air strikes conducted on Tudun Wulgo, Zari and Tumbun Alhaji, Kusuma, Sigir in Ngala and Arijallamari, in Abadam, Marte and Ngala Local government Areas, led to the killing of top ISWAP Leaders.

“The commanders that perished in the airstrikes include Mohammad Fulloja, Ameer Mallam Bello, Ba’a kaka Tunkushe, Abu Muktar Al -Ansari, Ameer Abba Kaka, Abu Huzaifa, Ameer Modu Kwayem, while Goni Mustapha who was the Chief Imam of the ISWAP escaped with bullet wounds.”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *