fbpx
Thursday, September 23
Shadow

Mun kashe sojojin Najeriya 10 a harin da muka kai Rann>>ISWAP

Kungiyar ISWAP data balle daga Boko Haram ta yi ikirarin kashe sojojin Najeriya 10 a harin da ta kai garin Rann dake karamar hukumar Kalabalge ta jihar Borno.

 

ISWAP dai ta kori sojoji daga garin inda jama’a ma suka rika tserewa amma daga baya, bayan awanni 8, sojojin sun koma suka kwato garin.

 

A bangaren sojin, sun bayyana cewa, Soja 1 da Dan Bijilante 1 ne suka rasa rayukansu a harin.

 

Saidai rahoton Daily Nigerian ya ruwaito wata murya daga kungiyar ISWAP din na cewa ta kashe sojoji kusan 12 inda ta jikkata wasu, yayin da wasu kuma suka tsere.

 

Hakanan sun yi ikirarin cewa, sun samu ganimar makamai da sauran kayan yaki.

“With Allah’s grace, we have killed 10 Nigerian soldiers, wounded many, while the rest ran away in Rann, Borno State.

“The spoils of war we got three devices, many arms and ammunition”, it read.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *