fbpx
Monday, November 29
Shadow

Mun Samu Ci Gaba Duk Da Rufe Kan Iyakokin Najeriya>>Nijar

Jami’an kula da karbar haraji a Jamhuriyar Nijar sun ce sun samu nasarori wajen tattara kudaden harajin shekarar da ta gabata.

Hukumomin sun ce an samu ci gaban ne duk da irin gibin da matakin rufe iyakokin Najeriya ya janyowa asusun gwamnati a kwanakin baya.
Yayin wata zantawa da Muryar Amurka, Magatakardan kungiyar jami’an haraji, Moussa Oumarou, ya ce, biliyan 500 na cfa suka yi nasarar karbowa daga hannun talakawa da sunan haraji a bara kadai.
Hakan kuma a cewarsa, na nuni da cewa an samu ci gaba sosai idan aka kwatanta da shekarun da suka shige.
“Najeriya, babbar kasa ce mai iyaka da yawa da Nijar, duk inda ka bi za ka iya shiga Najeriya, akwai kuma hadahadar kasuwanci tsakaninmu da Najeriya, wannan hada-hada da ake yi tsakaninmu, ta rage kudaden da ke shiga baitulmalin kasa,” a cewar Oumarou.
“Abin da muke fata, gwamnatin kasar Nijar da Najeriya, su tattauna tsakaninsu domin a samu maslaha,” ya kara da cewa.
VOAhausa.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *