fbpx
Thursday, December 2
Shadow

Mun tattauna matsalar tsaro da kuma sauke shuwagabanin jami’an Tsaro da Shugaba Buhari>>Sanata Lawal

Bayan ganawar da suka yi da shugaban kasa,Muhammadu Buhari,shugaban majalisar Dattijai, Ahmad Lawal ya bayyana cewa sun tattauna matsalar tsaron data shafi kasarnan ne da shugaban kasar.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Lawal ya shaidawa manema labarai dake fadar shugaban kasar cewa matsalar tsaro data sauke shuwagabannin jami’an tsaron ce suka tattauna.

Yace sun damu da matsalar tsaron kasarnan amma a matsayin shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya fi kowa damuwa da matsalar.

Yace sun tattauna akan batun kara samarwa da jami’an tsaron kayan aiki da suka hada da makamai da kuma inganta rayuwar jami’an data hada da lura da inda suke zama da makarantun da ‘ya’yansu ke halarta da sauransu.

Yace mutane kansu ‘yan kasa suna da rawar da zasu taka akan harkar tsaro.

Shima da yake magana da manema labarai, Shugaban majalisar Wakilai,Femi Gbajabiamila ya bayyana cewa a zaman da suka yi a majalisa sun kafa wani sabon kwamiti da zai rika duba harkar tsaron kasarnan daga lokaci zuwa Lokaci.

Ya bayar da tabbacin cewa za’a ga canji a harkar tsaron.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Ku biyomu a shafukanmu na sada zumunta dan samun labarai masu kayatarwa:

A shafin twitter zaku same mu a @hutudole

A shafin Facebook zaku samemu a @hutudolehausa

Danna nan dan sanin yanda zaku tallata hajarku a shafin hutudole

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *