fbpx
Thursday, September 23
Shadow

Muna da tsarin gamawa da ‘yan Bindiga gaba dayansu amma gwamnatin tarayya ke kawo mana cikas>>Gwamna El-Rufai

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa, suna da tsarin gamawa da ‘yan bindiga gaba dayansu.

 

Gwamnan ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a Channels TV wadda Independent ta ruwaito.

 

Gwamnan yace shine shugaban tsaro a jiharsa amma matsalar itace bashi da iko da jami’an tsaro sai umarnin da aka basu daga Abuja.

 

Gwamnan ya kara da cewa, amma suna samun hadin kai daga jami’an tsaron duk da yake cewa akwai abubuwan da suke so ayi amma ba’a yi ba.

 

Yace sabon yunkurin da aka dauka na yakar ‘yan Bindigar zai gama dasu gaba daya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *