fbpx
Wednesday, June 23
Shadow

Muna da yakinin Gwamnan Zamfara ba zai koma APC ba>>PDP

Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa tana da yakinin Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle ba zai koma jam’iyyar APC ba.

 

Kakakin jam’iyyar,  Kola Ologbondiyan ya bayyana haka inda yace babu me son ci gaban Najeriya da zai shiga APC lura da yanda jam’iyyar ta lalata al’amura a Najeriya.

 

Yace suna kokarin tattaunawa da gwamna Matawalle kan lamari. Saidai daga jihar Zamfara, Rahotanni na kara nuni da tabbacin komawar Gwamna Matawalle APC.

 

Wata majiya ta bayyanawa Independent cewa, Matawalle na APC ne kawai dai bai fito ya bayyana bane a hukumance.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *