fbpx
Tuesday, May 18
Shadow

Muna nan muna lissafin mutanen da ‘yan IPOB suka kashe mana, ko ta halin yaya sai mun rama>>Fulani

Kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah Kautal Hore ta bayyana cewa ba zata lamunci kisan da tsageran haramtacciyar kungiyar IPOB suke wa membobinta ba.

 

Kakakin Kungiyar, Saleh Alhassan ya bayyana haka inda ya ce suna nan suna lissafin yawan fulanin da ‘yan IPOB suka kashe.

 

Yace sun manta a lokacin yakin basasa Fulani sun rika basu mafaka a Arewa, yace yanzu an kashe musu mutane kusan 50 cikin wata daya.

 

Yace kuma zasu bi hanyar Doka data al’ada wajan daukar Fansa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *