fbpx
Sunday, September 19
Shadow

Musulmi ne ya kamata ya kara zama shugaban kasa a 2023>>Kungiyar kare muradun Musulmai ta Najeriya

Kungiyar kare muradun Musulmai ta Najeriya,  MURIC ta nemi cewa, Musulmi ne ya kamata ya kara zama shugaban kasar Najeriya.

 

Kungiyar na martanine ga maganar da kungiyar Kiristocin Najeriya,  CAN inda tace a 2023, Kirista ne ya kamata ya zama shugaban kasa.

 

Saidai a sanarwar da ta fitar ta bakin shugabanta, Fafesa Ishaq Akintola, MURIC ta bayyana cewa, sam hakan bai kamata ba, duk da dsi tana mutunta ra’ayin CAN din.

 

Muric tace Tsohon Shugaban kasa,  Olusegun Obasanjo yayi shekaru 8, inda Tsohon Shugaban kasa,  Goodluck Jonathan yayi shekaru 5 wanda idan an hada 13 kenan.

 

Yace Yar’adua yayi shekaru 2 yayin da shugaban kasa, Muhammadu Buhari yayi shekaru 8, yace dan haka idan za’a yi Adalci, musulmi ne ya kamata ya zama shugaban kasa a 2023.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *