fbpx
Saturday, December 4
Shadow

Musulunci Addinine me kyau: Ni rikakkiyar ‘yar casu ce, har giya na sha sosai amma musulunci yasa na nutsu

A baya Persephone Rizvi takan kwashe makonni tana sheke ayarta da holewa a wuraren fati, amma yanzu rayuwarta ta sauya. A wani bangare na sabon shirin BBC Three ta bayyana yadda musulunci ya ceci rayuwarta.

A lokacin da ina matashiya, na kasance ƴar taya ɓera ɓari.

Duk ƙarshen mako babu abin da muke yi sai casu. A kwanakin baya, haka ƙarshen mako na ke tafiya. Waɗanne kaya nake amfani da su? Sai mu zo batun shan barasa, sai kuma batun wa zai kai mu yawo cikin gari? Ba za a bar casewa ba har zuwa ƙarfe huɗu zuwa biyar na Asuba a gidan rawa, sai kuma daga baya a tafi casu a gida, a tashi da safe da marisar barasa.

Na tuna yadda nake faɗa da mata da yadda nake shan cigari.

Sai dai abin ya yi yawa. Dole ne abubuwa su saya.

Ina shan barasa matuƙa da kuma shiga damuwa da ba zan iya sanin me ma nake yi ba. Ina ƙoƙari na ga rayuwata tana da amfani kuma ina so rayuwata ta gyaru. Ni kaina ban san abin da muke yi.

Daga baya sai na Musulunta.

Na shiga cikin gida, Ni yanzu Musulma ce

Kafin na je jami’a, na yi wani aiki a ɓangaren amsa wayoyin kwastamomi a wani kamfani. Ɗaya daga cikin abokai na, Haleemah, Musulma ce. Na yi azumin watan Ramadan da ita, kuma shi ne karon farko da na san Musulunci sosai.

A lokacin ba na tunanin shiga Musulunci – ra’ayi na na ya sauya. ‘Raina yana raya mani cewa kwana 30 ana azumi, ba zan iya ba’.

A lokacin da nke azumin, ina ci gaba da zuwa casu da shan giya, sai dai daga baya ɗabi’u na sun sma sauyawa. Sai daga baya na fara irin wannan tunanin, “Na fi ƙarfin haka, na fi haka.” Watan da na yi azumin ya sa ina kama kaina da kuma godiya, da kuma bani damar kula da kaina da nake ta nema tun tuni. Abin da ya ja na ƙara rugumar Musulunci kenan.

Na tashi ina zuwa makaranta ranar Lahadi. Iyayena sun so ni da yar uwata mu san menene addini. Mahaifina baƙar fata ne amma na Birtaniya kuma yana zuwa cocin Kiristoci, sai kuma mahaifiyata tana so mu samu ilimin addini, amma ba su tilasta mu ba. Babu wani Musulmi a dangina.

A shekarar farko da na yi a jami’a, na ta gudanar da bincike ne a kan Musulunci, inda nake tunanin na Musulunta. Ina yawan zuwa Jam’ia da ke Salford da kuma dawowa gida wajen iyayena a Huddersfield, sai dai ba su san yadda nake son Musulunci a raina ba. Na bar abin a sirrance har sai wata rana da na shiga cikin gida da ɗankwali, “Irin ni Musulma ce yanzu!”.

Iyayena sun shiga ruɗani amma ba su nuna ba su ji daɗi ba. Sun ta tambayata kan abin da nake so, haka kuma suna so su san ko abin da nake so shi ne daidai.

Mahaifi na y ɗauka ɗokin da nake yi ya yi yawa ne, amma da gaske nake yi – Ina so na yi komai kamar yadda adinni ya ce ba tare ma da sanin fassarar Al-Qur’ani ba.

Ina so na yi komai da gaske.

‘Maza ba su damu na a yanzu, ina ɗaura ɗankwali’

Na jefar da jakar kayayyakina sakamakon ina ganin bana buƙataru kuma, na cire ƙumbunan da na saka sa’annan na sauya sunanan a kafafen sada zumunta, hakazalika na goge duk wasu hotunana na baɗala sa’annan na buɗe sabon shafi a Facebok ta yadda babu wanda zai gane ni.

Ina tunanin duka waɗannan kayayyakin na Turawa ne kuma haramun ne na saka su. Hakan ya sa nake ganin ba zan iya rayuwa a kusa da duk wani mai shan barasa ba haka kuma ba zan iya zuwa duk wani wuri da ake cakuɗe tsakanin maza da mata ba.

A wannan lokacin, ban fito na bayana wa mutane sosai yadda nake sabon addinina ba kuma ba na son ana yawan yi mani tambayoyi a kai.

A wajen Musulmi, mutane na da ra’ayoyinsu da kuma iyakokinsu kan ko za su ji daɗi su yi rayuwa a kusa da masu shan giya ko kuma irin kayayyakin da suke sakawa, amma ko a yanzu, na sauya ɗaurin kallabina da zai rufe har ƙirjina musamman ma idan akwai maza sosai a kusa,

Na fi samun natsuwa a yanzu a haka. Zan iya tafiya daga nan zuwa nan ba tare da wani ya tsayar da ni ba – yadda nake sa kaya a baya, ana yawan tsayar da ni. Idan zan yi tafiya ta minti goma, ana tsayar da ni aƙalla sau sau biyar. A yanzu maza ba su damu na kwata-kwata.

Ba wai ina cewa wannan matakin ba daidai bane, amma ba wai sun zo daga gare ni bane – Na yi tsalle ne na shiga. Kuma hakan na nufin abokaina da na sani a baya ba zan iya rayuwa da su ba a halin yanzu. Na ji kamar ni Musulma ce kuma ina ta ƙoƙarin yin rayuwa ta Musulunci amma ba su yi.

Ina a jami’a ne a lokacin da na karɓi kalmar shahada. Ban shirya yin hkan ba, amma na je Masallacin Eccles da ke Salford da kuma jerin tambayoyin da zan yi wa limamin.

Duk ya amsa tambayoyin inda ya ce ki maimaita abin da zan ce…. kuma na yi hakan inda daga baya ya taya ni murna da cewa a yanzu na Musulunta! Na ma rasa abin da zan yi amma daga baya na ji daɗi saboda daga ƙarshe burina ya cika.

Ƴan uwa Musulmai sun karɓe ni hannu bibbiyu. Na haɗu da ƙawaye kaɗan ta hanyar Musulunci – sun tuna mani abin da ƙawance a Musulunci yake nufi. Za mu iya magana da juna ba tare da ɓoye komai ba,.

Abokaina ne waɗanda suka ƙarfafa gwiwata kuma na zo na gane cewa duk shekara babu abin da ya kai irin mutanen da kake tare da su.

Na yi ƙoƙarin kawo ƙarshen rayuwata

Matan da kuke gani a fim, Twaheeda da Reema, su ne suka ƙara ƙarfafa mani gwiwa. Suna tuna mani cewa wannan duniya ba ita ba ce matabbata.

Kalmar YOLO da ke nufin sau ɗaya ake rayuwa, ban yarda da ita ba kuma ganganci ne!

Ban gane komai ba. Na sha komawa ruwa na shabarasa bayan na fita hayyacina, hakan bai kuma faruwa ba tsawon lokaci.

Tsayawata kai da fata domin ganin cewa na zama mutumiyar kirki ya tabbata a kullum. A yanzu ba ma na tunanin komawa ruwa kamar da.

Iyayena sun bani goyon baya – sun taya ni azumi na wasu lokuta. Babban abin damuwarsu shi ne ba zan taɓa komawa yadda nake a da ba, amma kamar yadda suka gani tsawo shekaru, har yanzu ni ce! Ina ba mutum girma da son zaman lafiya.

Daga shafin BBChausa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *