fbpx
Thursday, August 5
Shadow

Musulunci ya samu karbuwa, Me addinin gargajiya ya karbi shahada

Dan shekaru 78 me addinin gargajiya, Ezekiel Adekunle Eleede dake Okeho a jihar Oyo ya bar bautar gumaka inda ya karbi addinin Musulunci.

 

Ya zabi sunan Abdulsalam Adekule bayan da malamin Addini a jihar, Alhaji Daud ya bashi kalmar Shahada.

 

Da yake magana da manema labarai ya bayyana cewa bisa radin kansa ya shiga addinin Musulunci bayan da ya shafe shekaru 15 yana bautar gumaka amma basu amfaneshi da komai ba.

 

Yacebai taba zuwa coci ko masallaci ba tunda aka haifeshi amma yana farin ciki da shiga Addinin Musulunci.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *