fbpx
Thursday, September 23
Shadow

Mutane 169 sun mutu sakamakon barkewar cutar kwalara a jihar Kano

Daraktan Kiwon Lafiya, Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano, Dakta Ashiru Rajab ya bayyana cewa mutane 169 ne suka mutu sakamakon barkewar cutar kwalara a kananan hukumomi 41 daga cikin 44 na jihar.

Da yake magana da manema labarai, ya bayyana cewa an samu asarar rayuka cikin watanni uku a jihar.

A cewa shi, mutane 191 da suka kamu da cutar a halin yanzu suna karbar magani a cibiyoyin kiwon lafiya daban-daban a jihar.

Daraktan Kiwon Lafiyar ya ba da tabbacin cewa gwamnatin jihar tana yin duk mai yuwuwa don shawo kan lamarin.

Ya yi bayanin cewa jihar ta samu mutane 5,221 a cikin watanni ukun da suka gabata, yana mai cewa kusan 4,860 sun yi jinya kuma an sallame su.

Daraktan ya jaddada cewa gwamnatin jihar Kano ta fara gagarumin gangamin fadakarwa da wayar da kan al’umma, musamman mazauna karkara kan matakan da ake bukata don kula da tsabtar muhalli da na mutum don gujewa barkewar annoba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *