fbpx
Sunday, September 19
Shadow

Mutane 2 sun mutu, gidaje 1,500 sun lalace bayan ruwan sama me karfi a Katsina

Ma’aikatar bada agajin gaggawa ta jihar Katsina, SEMA ta bayyana cewa, ruwan sama da aka yi me karfi sosai ya lalata gidaje 1,500 da kashe mutane 2 a kananan hukumomin 3.

 

Kakakin hukumar, Alhaji Umar Muhammed ne ya bayyana haka inda yace kananan hukumomin Sabuwa, Bindawa, da Faskarine abin ya fi shafa.

 

Yace mutane 2 da suka mutu sun fito ne daga karamar hukumar Bindawa.

 

Yace suna kokari dan ganin an tallafawa wanda lamarin ya shafa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *