fbpx
Monday, November 29
Shadow

Mutane 3 sun mutu a wani mummunan hatsarin mota a jihar Kwara

Mutane uku ne suka rasa rayukansu a wani mummunan hatsarin mota da ya afku a garin Otte da ke kan babbar hanyar Ilorin zuwa Ogbomoso a ranar Asabar.

Wasu da dama sun jikkata a hatsarin motan.

Motocin guda biyu da hadarin ya rutsa da su, Mistibushi dauke da wata mota kirar Toyota Corolla sun yi karo da juna, kamar yadda shaidun gani da ido suka bayyana.

An bayar da rahoton cewa mutanen uku da abin ya shafa sun mutu a nan take.

An tattaro cewa motar ta fito ne daga Ilorin, yayin dayan motar ta nufo wata hanya.

Kwamandan sashin na hukumar kiyaye haddura ta kasa FRSC, Jonathan Owoade ya tabbatar da faruwar hatsarin lokacin da aka tuntubi shi ta wayar tarho ranar Asabar.

Owoade ya ce an kai wadanda suka jikkata zuwa babban asibitin jihar, dake Ilorin, yayin da aka ajiye gawarwakin a dakin ajiyar gawa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *