fbpx
Monday, May 10
Shadow

Mutane bakwai sun mutu a hatsarin mota a Legas bayan da suka yi mankas da giya

Hukumar Kiyaye Hadurra ta Tarayya (FRSC) ta bayyana cewa mutune bakwai ne suka mutu a safiyar jiya a hatsarin mota da ya faru kan titin Lekki-Epe Expressway.

Hatsarin wanda ya afku ne da misalin karfe 1 na dare.

Wadanda suka mutu sun hada da; maza biyu da mata biyar, suna tafiya ne a cikin Lexus Sports Utility Vehicle (SUV) kuma ana zargin cewa suna cikin mayen giya a lokacin hadarin.

An ce Direban motar kirar SUV ya rutsa cikin wata babbar motar da ke tafiya, wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwar dukkan mutanen da ke ciki.

A cikin wata sanarwa, Jami’in Ilimin Jama’a na FRSC (PEO) a Lagos, Route Commander Olabisi Sonusi ya ce an kwashe gawarwakinsu zuwa dakin ajiye gawa.

Da yake nakalto jawabin shugaban hukumar FRSC na jihar, Kwamandan rundunar Corps Olusegun Ogungbemide, Sonusi ya shawarci masu ababen hawa da su guji shan giya. ”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *