fbpx
Monday, October 25
Shadow

Mutane biyar sun mutu a wani hadarin mota a jihar Jigawa

An tabbatar da mutuwar mutum biyar, yayin da wasu suka samu munanan raunuka a wani mummunan hatsarin mota a karamar hukumar Taura, jihar Jigawa.

Wani ganau ya shaidawa manema labarai cewa hatsarin ya faru ne a ranar Talata a arangama, wanda ya hada da motar Golf 3 guda biyu a kauyen Nomi, a kan hanyar Kano zuwa Gujungu a karamar hukumar Taura.

Kakakin hukumar tsaron  Civil Defence, CSC Adamu Shehu ya tabbatar da faruwar lamarin.

A cewarsa, mummunan hatsarin mota ya shafi motar Golf 3 da wani Alh. Kabiru Muhd, mai shekara 55 wanda ke zuwa daga Gujungu zuwa Taura da wata Golf 3 da Kailua Saudi mai shekara 45 na kauyen Kiri wanda ke zuwa daga Kano zuwa Gujungu.

Ya bayyana cewa lokacin da suka isa kauyen Nomi a Taura, sun yi karo da juna wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyar, ciki har da Malam Sallau mai shekaru 60 da Zulyadaini Muhammad mai shekaru 65, yayin da sauran gawarwakin uku har yanzu ba a kai ga tantancesu ba.

Kakakin NSCDC ya kara da cewa wadanda suka samu raunuka daban -daban an garzaya da su zuwa babban asibitin Ringim don yi musu magani, yayin da aka ajiye sauran gawarwakin wadanda ba a san ko su waye ba a dakin ajiyar gawarwaki a wannan asibiti.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *