fbpx
Wednesday, April 21
Shadow

Mutane goma sun mutu, yayin da wasu goma sha biyu sun ji rauni a hatsarin mota a Bauchi

Mutum 10 ne aka tabbatar da mutuwarsu a wani hatsari a ranar Asabar a Azare, karamar Hukumar Katagum, Jihar Bauchi.
Mista Yusuf Abdullahi, Kwamandan sashen na Hukumar Kiyaye Haddura (FRSC) a jihar Bauchi, wanda ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai ya ce hatsarin wanda ya faru da misalin karfe 2:30 na rana ya kuma bar wasu 12 da munanan raunuka.
Ya yi bayanin cewa hatsarin ya faru ne a lokacin da wani babur dauke da fasinjoji hudu ya kutsa kai cikin wata motar bas din Toyota Hiace mai shigowa ta Gombe line.
A cewarsa, fasinjojin da ke kan babur din sun rasa rayukansu nan take.
Abdullahi ya ce mutane shida kuma sun rasa rayukansu a cikin motar sannan kuma an kai gawarwakinsu zuwa asibitin lafiya na tarayya (FMC), Azare.
Ya ce wadanda suka jikkata an kai su asibitin New Jama’are da ke Azare domin yi musu magani.
“An kira mutanenmu a garin Azare kuma sun hanzarta zuwa wurin kuma sun ceci wadanda lamarin ya rutsa da su zuwa asibiti inda wani likita ya tabbatar da mutuwar mutane 10, hudu a kan babur da kuma shida a cikin bas din,” in ji Kwamandan Sashin na FRSC.
“Daga cikin mutane 12 da suka jikkata, muna da manya maza shida, mata manya uku, yaro daya namiji da yara mata biyu,” in ji shi.
Abdullahi ya danganta hatsarin da wuce gona da iri da direban motar Gombe Line ya yi, ya kara da cewa dan acaban ya tsallaka titin motar sai ya fadi kasa tare da fasinjojinsa.
Ya shawarci direbobi su himmatu wajen girka na’urar don takaita hadurran da ke faruwa a kan hanyoyi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *