fbpx
Saturday, October 16
Shadow

Mutane hudu sun mutu, yayin da motar bas mai kujeru 18 ta fada cikin Kogin Niger a jihar Kogi

Akalla mutane hudu ne aka tabbatar sun mutu a lokacin da wata motar bas mai kujera 18 ta nutse cikin kogin Niger a yankin Koton Karfe na jihar Kogi.

An tattaro cewa an ceto wasu mutane 13 da ransu yayin da mutum guda ya bace a hadarin.

Hatsarin ya faru ne da misalin karfe 7:30 na daren ranar Talata lokacin da direban bas din ya yi bacci kuma ya rasa yadda zai yi, inda ya fada cikin kogin.

A cewar kwamandan rundunar tsaro ta NSCDC, Suleiman Mafara, wanda ya bayyana hakan ga manema labarai a Lokoja, a lokacin da ya samu kiran gaggawa, mutanen sa na bagaren Bala’i da Rikicin a Titin Tarayya. An tura jami’an tsaro da masu aikin sa kai zuwa wurin.

Ya kara da cewa mutanensa da sauran Jami’an tsaro suna aiki ba dare ba rana don gano mutum guda daya tilo da har yanzu ba a tantance ba.

Mafara ya bayyana cewa an ajiye gawar a dakin ajiye gawa a Lokoja.

Kwamandan NSCDC, duk da haka, ya gargadi direbobi da matafiya da su bi ƙa’idodin aminci na hanya don hana kashe -kashe a kan manyan hanyoyi.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *