fbpx
Sunday, September 19
Shadow

Mutane Miliyan 8 ne suka amfana da tallafin kawar da Talauci da gwamnatina ke bayarwa>>Shugaba Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce gidaje miliyan 1.6 da ƴan Najeriya miliyan takwas ne ke amfana da tallafin kudi da gwamnatinsa ke bayarwa domin rage raɗaɗin talauci.

Cikin sanarwar da fadar shugaban ta fitar a ranar Talata, Buhari ya ce ƙoƙarin da gwamnatinsa ke yi na rage talauci a Najeriya na ci gaba da bunƙasa.

Sanarwar ta ce Buhari ya faɗi haka ne a bikin buɗe taron shekara-shekara na harakokin banki da kuɗi na cibiyar horar da ma’aikatan banki ta Najeriya.

A cikin jawabinsa a cewar sanarwar, shugaban ya ce rajistar talakawa da aka yi da marasa galihu ta ƙunshi mutum miliyan 32.6 daga gidaje miliyan 7 na masu ƙaramin ƙarfi.

Ya kuma roƙi bankuna su taka muhimmiyar rawa wajen inganta rayuwarsu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *